MDD za ta yi nazarin daftarin da Rasha ta shigar game da syriya
January 17, 2012Ƙasar Rasha ta shigar da wani sabon daftarin doka gaban kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya game da rikicin siyasa da ake fiskanta yanzu haka a ƙasar Syriya. Sai dai jakadun ƙasashen yammacin duniya sun soki wannan daftari a inda suka ce ba ya tir da amfani da ƙarfi fiye da kima da shugaban Bashar al-Assad ke yi akan masu boren ƙin jinin gwamnati. Kana sun zargi fadar mulkin Moscow da ƙin bayyana hanyoyin da ya kamata a bi domin kawo ƙarshen wannan rikici da ya haddasa asarar rayukan mutane dubu biyar.
Sai dai ƙasar Amirka da kuma ƙawayenta na Turai sun yaba matakin na Rasha, wanda suka danganta da ci gaba mai ma'ana, tare da miƙa bukatar gyara ga daftarin. Ƙwararru da sauran mambobin kwamitin na Majalisar za su yi nazarin daftarin na Rasha a wannan talata a birnin New-York.
A ɗaya hannun kuma, Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta amince za ta horas da tawagar sa ido da ƙungiyar haɗin kan larabawa ta tura ƙasar ta Syriya. Wani kakakin majalisar ya bayyana wa manaima labarai a birnin New-York cewa horon zai fara ne cikin 'yan kawanaki masu zuwa. Wannan tawaga ta ƙasashen larabwa ta yi ta shan suka game da gaza kawo ƙarshen gallazawa masu fafutika da gwamnatin Syriya ke yi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu