MDD ta yi tir da niyyar Jamus na mayar da 'yan Afghanistan
July 4, 2025Majalisar Dinkin Duniya ta soki lamirinJamus dangane da aniyyarta ta korar 'yan Afganistan da ke samun mafaka zuwa kasarsu ta asali, wanda ministan cikin gida Alexander Dobrindt ya yi dogon bayani a kai. A wani taron manaima labarai da ta gudanar a birnin Geneva, mai magana da yawun hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta ce bai dace a mayar da mutane kasar Afganistan ba, duba da halin da kasar ke ciki na take hakkin bil'adama, ciki har da kisan ba gayra.
Karin bayani: Taliban ta haramta wa jami'in MDD shiga Afghanistan
Ita dai Jamus, tana tunanin yin shawarwari kai tsaye da mahukuntan Taliban da ke mulkin Afganistan don saukaka mayar da 'yan kasar da ke aikata manyan laifuka. Sai dai kasancewar Jamus kamar yawancin kasashe na duniya, ba ta amince da gwamnatin Taliban a matsayin halaltacciya ba, tana hulda da 'yan Taliban ne ta hanyar wasu kasashe. Amma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD na ci gaba da ba wa kasashen duniya shawarar kauce wa mayar da 'yan Afghanistan kasarsu ta asali.