Guterres: Gargadi kan shiga rikicin Iran da Isra'ila da soji
June 18, 2025Talla
Ita ma kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bukaci bangarorin biyu, da su kare fararen hula yayin da adadin mace-mace da jikkata ke ci gaba da karuwa.
Babbar sakatariyar kungiyar ta kasa da kasa Agnes Callamard wadda ta yi wannan kira, ta bukaci Iran da Isra'ila da su martaba hakkokin jama'a, tare da tabbatar da cewa ba fararen hula a kasashen biyu ne ake gasa wa tsakuwa a hannu sakamakon wannan rikici ba.
Rikicin dai ya fara ne a ranar Juma'a, lokacin da Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin harin bama-bamai wanda ya sanya Iran mayar da martani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.