MDD ta yi gargadin barkewar yunwa a Sudan ta Kudu
June 12, 2025Wasu hukumomin Majalisar Dinkin Duniya uku sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar barkewar yunwa a wasu sassan kasar Sudan ta Kudu da tashe-tashen hankali ya yayyaga.
Hukumar Abinci da ta Noma da kuma Asusun kula da Kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya suka ce mutane daga yankuna 11 cikin 13 na jihar Upper Nile ta Sudan ta Kudu suna bukatar abinci da gaggawa.
Sudan ta Kudu: Sama da mutum dubu 165 000 sun yi kaura
Jihar ta kasance fagen daga tsakanin dakarun gwamnati da kuma 'yan tawaye masu dauke da makamai wadanda ke adawa da gwamnatin shugaba Salva Kiir.
Yaki tsakanin bangarorin biyu ya yi matukar zafi a watannin nan inda aka lalata gidaje da kuma wuraren kasuwanci tare da yin katsalanda ga harkokin jinkai a cewar sanarwar da hukumomin uku suka sanya wa hannu.
Kwamitin Sulhu na MDD ya bukaci kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu
Mutane akalla 32,000 suna fama da wata irin yunwa da hukumomi suka bayyana a matsayin ta fitar hankali kuma halin da suke ciki a yanzu ya fi muni idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a baya.