MDD ta rage shirin agajin jin kai saboda karancin kudi
June 16, 2025Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa za ta rage yawan taimakon jin kai da take bayarwa sakamakon matsalar karancin kudi mafi muni da take fuskanta. Sai dai wannan matsayin zai kara dagula halin da dubban miliyoyin mutane ke ciki a fagen rikice-rikice a wannan shekarar. Matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na kawo karshe ko rage tallafin da Amurka ke bayarwa ne ya jefa daukacin sassan duniya cikin rudani, inda kudin ya zama kaso mai tsoka na kasafin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ko kungiyoyi masu zaman kansu daban-daban.
Wata sanarwa da hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD OCHA ta fitar ta bayyana cewar ta yi nasarar tara dala biliyan 5.6 ne kacal daga dala biliyan 44 da aka nema da farko,domin kula da jin kai a Sudan, Gaza, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Bama, da Ukraine.