MDD ta nuna bacin rai kan kashe matasan Kenya a zanga-zanga
June 26, 2025Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa dangane da matakin da jami'an tsaron Kenya suka dauka na amfani da karfi wajen harbe masu zanga-zanga har lahari a Nairobi babban birnin kasar, inda ta yi kira da a kwantar da hankula. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kakakin ofishin Hukumar Kare Hakkin bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Elizabeth Throssell, ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike "don gurfanar da wadanda ke da hannu a harbe-harben gaban kuliya."
Karin bayani: Arangama ta barke a Kenya tsakanin 'yan sanda da matasa
Gwamnatin Kenya na shan suka daga kungiyoyin kare hakkin bil Adama ciki ha da Amnesty International, bayan da mutane 16 suka mutu yqayin da fiye da 400 suka samu raunuka a zanga-zangar. Sai dai fadar mulki ta Nairobi ta kare kanta inda ta yi ikirarin murkushe wani abin da ta kira juyin mulki da aka kitsa mata. Wannan ne shekara ta biyu a jera da matasan Kenya ke zanga-zangar kalubalantar gwamnati a kan tsadar rayuwa da rashin aikin yi.