MDD ta kadu kan yawan mutane da ke bukatar agaji a Gaza
May 27, 2025Majalisar Dinkin Duniya ta ce bidiyon da ya nuna dubban Falasdinawa sun yi fitar dango domin karbar kayan agaji a Gaza abu ne mai matukar sosa rai.
Mai magana da yawun Majalisar ta Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya fada wa manema labarai cewa majalisar da kuma abokan huldarta sun samar da wani tsari mai kyau na kai wa mabukata tallafi a Gaza.
MDD ta yi tir da harin Isra'ila a Gaza da ya rutsa da jami'anta
A cewar babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ayyukan jinkai suna da matukar muhimmanci wajen dakile yunwa da kuma fitar da farar hula cikin wahala a duk inda suke.
Dubban mutane ne dai suka tuttuda zuwa wata cibiya ta raba kayan agaji mai samun goyon bayan Amurka a ranar Talata a kudancin Gaza don karban agajin.
Gaza: Amurka ta mika wa MDD daftarin tsagaita wuta
A cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar, ta ce mutane da suka halarci wurin rabon kayan agajin sun fi karfin abin da ta zata.