MDD ta ce yakin Sudan zai iya shiga Afirka ta Tsakiya
June 27, 2025Hukumar da ke kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a game da yiwuwar yaduwar rikicin Sudan zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda zai iya kawo cikas ga sabon yanayin zaman lafiya da ake kokarin kafawa a kasar, ciki har da ayyukan sojojin 'yan sanda na musamman.
A makon da ya gabata, wata kungiyar masu gwagwarmaya da makamai ta kai hari kan wata rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda aka kashe wani dan sandan kiyaye zaman lafiya dan asalin kasar Zambiya.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, guda daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, tana da iyaka da Sudan, wadda tun cikin watan Afrilu 2023 take cikin rikici mai tsanani tsakanin sojojin gwamnati da rundunar mayakan ko ta kwana ta RSF.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fuskantar karuwar yawan 'yan gudun hijirar Sudan da ke tserewa daga rikicin, inda rahoton MDD ya kiyasta cewa akwai kimanin sama da 'yan gudun hijira dubu 36 a kasar a halin da ake ciki.