LafiyaNa duniya
MDD: An sami karuwar cutar Kyanda
April 24, 2025Talla
Kungiyar lafiya ta duniya WHO da asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun ce an sami karuwar cutattukan kyanda da sankarau da kuma shawara.
Rage tallafin kudi da yada labaran kanzon kurege da kuma halin tagaiyarar al'umma sun kara ta'azzara lamarin.
Sanarwar hadin gwiwa da hukumomin suka bayar ta ce an ceto rayuwar mutane kimanin miliyan 150 sakamakon alluran riga kafi a cikin shekaru 50 da suka gabata.