MDD: Dakarun Kwango da M23 sun aikata laifukan yaki
September 6, 2025Talla
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya gano tarin laifuka take hakkin bil Adama da dakarun kwango da 'yan tawayen M23 suka aikata a rikicin gabashin Kwango. Shugaban hukumar kare hakkin 'dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya bayyana laifukan da aka zayyana dalla-dalla a cikin rahoton a matsayin abin tashin hankali. Wannan dai shi ne karon farko da rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana cin zarafi a Kwangon a matsayin laifukan yaki.
Karin bayani: Yaushe mata za su tsira daga mayakan M23?
Rahoton ya ce, 'yan tawayen M23 sun azabatar da mutane tare da batar da wasu yayin da suka rika daukar yara a matsayin mayakansu. A cewar rahoton, kungiyar ta kuma ci zarafin mutane ta hanyar yin fyade musamman ga mata.