Mayarwa da 'yan tawayen Libiya kuɗaɗen Gaddafi
August 29, 2011A dai halin da ake ciki yanzu babu wani musu a game da cewar kwamitin mulkin da 'yan tawaye suka naɗa a Libiya, ya mayar da dukkan al'amuran ƙasar ƙarƙashin ikonsa, duk da cewar har yau ba a sake jin ɗuriyar madugun juyin-juya-halin ƙasar Muammar Gaddafi ba da kuma cewar har yau magoya-bayansa ba su ba da kai bori ya hau kwata-kwata ba. Sai dai kuma 'yan tawayen sun dage akan lalle sai an danƙa musu dubban miliyoyin kuɗin man da Gaddafi ya ajiye a ƙetare. Amma kuma ƙwararrun masana na saɓani akan ko a haƙiƙa ya dce a miƙa wa 'yan tawayen waɗannan kuɗaɗen tun a yanzun.
Bisa ga dukkan alamu dai ba za a iya tantance yawan kudaɗen da Gaddafi ya ajiye a ƙetare tsawon mulkinsa na shekaru 42 ba. An dai ƙyasce cewa yawansu zai kai dalar Amirka miliyan dubu 150. Aƙalla an samu ikon gano wani ɓangare na waɗannan kuɗaɗe aka kuma ɗora hannu kansu. A kuma halin da ake ciki yanzu kwamitin mulkin riƙon ƙwarya na Libiya na neman da a maido masa da waɗannan kuɗaɗe. Bisa ga ra'ayin Markus Kaim shugaban sashen nazarin manufofin tsaro a gidauniyat kimiyya da siyasa dake Berlin, wannan buƙatar haƙƙinsu ce:
"Muhimmin abin da ake buƙata a Libiya a yanzun shi ne kuɗin gudanar da ayyukan sake gina ƙasar. A ɓangare guda dai Libiya, bisa la'akari da arziƙin mai da na gas da take da shi, ƙasa ce mawadaciya, sannan a ɗaya ɓangaren kuma akwai wasu muhimman abubuwan guda biyu da ƙasar ke buƙata dangane da ayyukan sake ginawa a cikin makonni masu zuwa, waɗanda su ne tabbatar da tsaro da ƙirƙiro kafofi na siyasa."
Amma fa Hamadi El-Aouni mai koyar da kimiyar siyasa da tattalin arziƙi a jami'ar Berlin na tattare da ra'ayi ne dabam. A ganinsa da tuntuni ya kamata a danƙa wa gwamnatin riƙon ƙwarya kuɗaɗen na Gaddafi:
"Tun da jimawa kwamitin mulkin na ƙasa ke buƙatar waɗannan kuɗaɗe. An fuskanci ƙarancin kuɗi wajen biyan jami'an gwamnati da ma'aikata da kuma biyan wasu muhimman kayan buƙatun yau da kullum. A gani na an makara ƙwarai da gaske, kuma wajibi ne a hanzarta a yanzun."
Kawo yanzun dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta saki dala miliyan dubu ɗaya ne da ɗari biyar na kuɗaɗen Gaddafi da Amirka ta ɗora hannu kansu. Ita ma Italiya tuni ta ba da sanarwar cewar zata miƙa wa 'yan tawayen Euro miliyan 350. Amma fa hakan ba da banza ba, in ji Markus Kaim, wanda ya ƙara da cewar:
"Dangane da Italiya da wasu ƙasashen maganar ta shafi kasancewa ne a cikin cikakken shiri dangane da sabbin kwangilolin da za a sake tattaunawa kansu, musamman ma dai a game da haƙan mai da gas a Libiya. A wannan ɓangaren wasu ƙasashen na fatan ganin kamfanoninsu sun ci gajiyar lamarin."
Amma ita ƙungiyar tarayyar Turai tana ci gaba da ɗariɗari a game da sakin dubban miliyoyin da Gaddafi ya ajiye a ƙasashenta. Joachim Hörster, wakili a kwamitin kula da manufofin ƙetare na Jamus kuma ƙwararren masani kan al'amuran yankin gabas ta tsakiya, ya bayyana dalilin haka yana mai cewar:
"Mai yiwuwa ana buƙatar kuɗi ruwa a jallo dangane da wasu ɓangarori na musamman, misali dai sayen kayan masarufi ko samar da wutar lantarki. Amma babban abin da ake buƙata shi ne ya kasance ana da kafofin da zasu aiwatar da kuɗaɗen daidai yadda ya kamata a ƙasar Libiya. Wannan ita ce ayar tambayar da ya kamata a fara amsata, sannan a san irin matakin da zai biyo baya."
Aihin wannan dalilin ne ya sanya ƙasashe da dama ke ɗariɗari game da danƙa wa 'yan tawayen kuɗin. Sun fi ƙauna su jira har sai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da haske game da yin hakan tukuna. Wannan ma shim ne ainihin matsayin da Jamus ta ɗauka a halin yanzun.
Mawallafi: Thomas Latschan/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Muhammed Nasiru Awal