Mayakan RSF sun kwace muhimman garuruwa a Sudan
May 30, 2025Mayakan RSF da ke yaki da sojin Sudan sun yi ikirarin kame wasu muhimman garuruwa a kasar mai fama da yaki da kuma cutar kwalarar da ta halaka mutane akalla 70 a makonnan.
Sama da shekara uku kenan kasar Sudan da ta kasance ta uku a girma a nahiyar Afirka ta fada rudani biyo bayan yaki tsakanin dakarun RSF da kuma sojin Sudan da Janar Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta.
Mayakan RSF na ci gaba da halaka 'yan gudun hijira a lardin Darfur
Mayakan na RSF suka ce sun kame Dibeibat, da ke kudancin jihar Kordofan sai kuma Al-Khoei da ke jihar Kordofan ta yamma.
Dama sojojin Sudan ne ke da iko da garin na Al-Khoei da ke da nisan kilomita kusan 100 daga birnin El-Obeid da kuma ya kasance hanyar zuwa birnin Khartoum.
Farmakin RSF a Port Sudan ya dauki hankalin jaridun Jamus
Rikicin na bangarorin biyu dai ya raba Sudan gida biyu inda sojin kasar ke iko da tsakiya da gabashi da kuma arewacin kasar sai kuma RSF da ke iko da kusan dukkan Darfur da ke yammaci da kuma wasu sassan kudancin kasar.