Mayakan RSF sun halaka 'yan gudun hijira 481 a Darfur
April 28, 2025Talla
Dakarun Rapid Support Forces (RSF), wadanda ke cikin mummunan yaki da sojojin Sudan tun a watan Afrilun 2023, sun kai hari da alburusai da bindigogi a sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da ke kusa da El-Fasherbabban birnin lardin Darfur.
A cikin 'yan makonnin nan, mayakan na RSF sun tsananta kai hare-hare kan wannan yankin da ke zama na karshe a Darfur da har yanzu ke karkashin ikon sojojin gwamnati, da sansanonin 'yan gudun hijirar da ke kewayen Abu Shouk da Zamzam.
MDD ta ce hare-haren na mayakan RSF a arewacin Darfur ya halaka mutane akalla 481 cikin makonni biyun da suka gabata.