Matsayin Turai kan takunkumin Zimbabwe
July 23, 2012A zaman taron ministocin ƙasashen waje na tarayyar turai, ƙasashen sun bayyana matsayinsu a dan gane da takunkumin da suka lakabawa ƙasar Zimbabwe tun a wancan lokacin, waɗanda suka haɗa da katse bada talafi ga ƙasar da kuma hana wa wasu jami'an gwamnatin su 112 shiga cikin ƙasashen Tarayyar Turan. Wannan matakin da ƙungiyar turan ta ɗauka na sasauta takunkumin, ya biyo bayan sharuɗɗan da suka gindaya wa hukumomin ƙasar ne na su shirya zaɓen raba gardama tsayayye wanda zai ɓullo da sabon kundin tsarin milki wanda kuma zai ɗora ƙasar bisa tafarkin demokraɗiya na gari tun bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaba Robert Mugabe da ɗan adawa kuma praminista Morgan Tsvangirai a shekara ta 2008.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Abdullahi Tanko Balla