Tasirin sojojin hayan Rasha a Afirka
March 17, 2025Shekaru da yawa, abubuwan da suka faru sun kasance kamar ba za su iya sauyawa ba: Sojojin haya na Rasha sun sami gindin zama a yawancin kasashen Afirka. A lokaci guda, sun samu damar samun albarkatun ƙasa masu mahimmanci kamar zinariya da katako na wasu yankuna na Afirka.
Karin Bayani: Mali: Ko yakin Rasha da Ukraine na fadada?
Sai dai labarin nasarar Rasha ya fara nuna alamun wargajewa. A watan Yulin shekarar ta 2024, sojojin hayar Rasha sun yi asara mai yawa lokacin da 'yan tawayen Abzinawa suka yi musu kwanton bauna a kusa da garin Tinzaouatène da ke arewacin Mali. Lamarin ya kasance babban batu a Afirka, haka lokacin da gwamnatin Bashar Al-Assad ta ruguje a Syriya a watan Disamba Rashar ta rasa tasirinta. Martaba da kimar sojojin Rasha ta zube a ido jama'a saboda ci gaba da samun rahotannin take hakkin dan Adam daga sojojin haya na Rashar
Shin ta yaya za a iya dakile tasirin sojojin haya na Rasha?
Wani bincike na baya-bayan nan da kungiyar Global Initiative da ke yaki da aikata laifuffukan ta kasa da kasa wato (GI) ya ba da haske kan ayyukan sojojin hayar Rasha a Afirka sannan ya ba da shawarar yadda za a iya dakile Rashar
Da farko ware yankunan da sojojin Rashar suke ta hanyar mayar da su saniyar ware
• Matsin lamba na diflomasiyya kan abokan huldar Rasha
• Haɗin kai na kasashe na takunkumi a kan sojojin haya na Rasha
Matakai na yaki da labaran karda kanzon kurege na farfaganda na Rasha
• Daina bayar da tallafin na karfafa tattalin arziki wa kasashen da ke hulda da Rashar
Kasahen yankin Sahel da suka hada da Mali, da Burkina Faso da Nijar suka fice daga kawancen tattalin arzikin ECOWAS bayan juyin mulkin da sojoji suka yi tare da kafa kawancen kasashen yankin Sahel AES ba su ba da hadin kai ga sauran kasashen dunia
Kwararru na gani ya zama wajibi kasahen duniya su yi aiki da wadannan kasashe inda har ana son cimma nasara wadanda suke ganin sai an kiyaye wasu hanyoyin sadarwa, musamman a fannin tsaro da karfafa hulda da kasashen na Sahel saboda a wannan fanin domin samun abin da ake so. Masana dai na ganin idan har Rasha ta amince aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a yakin da take da Ukraine watakila za a samu sauki na fadadar sojojin haya na Rashar a cikin kasahen Afirka, yayin da makomar Rasha a Afirka ita ma ta dogara da yakin Ukraine.