Matsayin Jamus kan murda zaben Rasha
December 5, 2011Talla
Kasar Jamus ta bayyanar da damuwarta game da rahotonnin da ke nuni da tafka magudi a zaben majalisar dokokin da ya gudana a kasar Rasha. A cewar kakakin shugabar gwamnati Angela Merkel, Jamus ta bukaci a yi bayani game da wannan zargi a cikin limana. Jami'an sa ido na kungiyar tsaro da hadin-gwiwar kasashen Turai da kuma taron majalisar Turai sun ce yakin neman zaben ya gudana ne a cikin yanayi na rashin adalci. Sun kuma kara da cewa an yi murdiya da satan kuri'u. Jam'iyyar fraiminista Vladimir Putin ta lashe zaben amma tare da hasarar rinjayen da take da shi a majalisa. Wannan zabe zai share fagen aiwatar da musayar mukamai da ake shirin yi tsakanin Putin da Dmitri Medvedev.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal