Matsalolin zaɓe a Nijar
January 12, 2011Talla
A zaɓukan gundumomi da na ƙananan hukumomi a janhuriyar Nijar ana ci gaba da fama da matsaloli sakamakon ƙarancin kayan aiki da ake fuskanta, abin da ya kai ga dakatar da zaɓen ma gaba ɗaya ko kuma ɗage su a wasu yankunan ƙasar. To sai dai kuma duk da haka tun abin da ya kama daga yammacin yau ne ake sa ran fara sakamakon zaɓukan a wuraren da aka samu kafar gudanar dasu.
A halin yanzu hukumar zaɓe mai zaman kanta a ƙasar ta Nijar ta fara bayyana sakamakon wucin gadi na zaɓukan. Ana iya sauraron rahotannnin daga wakilanmu Gazali Abdou Tasawa a Yamai da kuma Salissou Boukari a Tahoua a can ƙasa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Ahmad Tijani Lawal