Matsalolin jigilar mahajjata a Nijar
September 19, 2012
A jamhuriyar Nijar wa'adin da hukumomin kasar
Saudiyya su ka baiwa kasashe domin isar da maniyyatansu don sauke
faralin shekarar bana, ke ci gaba da kurewa kampanonin shirya aikin
hajji na kasar sun soma bayyana fargabarsu a game yiwuwar kasa kai
maniyatan kasar ta su akan lokaci. Kamfanonin shirya aikin hajjin na
kasar Nijar sun bayyana cewa suna fuskantar jerin wasu matsaloli da su
ka hada da rashin jirgi da kan yin barazana ga aikin jigilar maniyyatan
kasar zuwa kasar ta Saudiyya a shekarar bana.
A ranar 22 ga watan Octoba mai zuwa dai ne wa'adin da hukumomin kasar
Saudiyya su ka baiwa kasashe domin isar da maniyyatansu ya ke kawo
karshe. Tuni kuma wasu kasashe su ka dau haramar soma jigilar maniyatan
na su zuwa kasa mai tsarki. Saidai a Jamhuriyar Nijar duk da ikirarin
da hukumomi su ka yi na kawo karshen irin daburtar da aka yi ta
fuskanta cikin tsarin shirya aikin hajjin shekaru da dama ga bisa
dukkan alamu dai ko a bana yar bara ce, inda yanzu haka jerin wasu
matsaloli su ka zo su ka dabaibaye shirin aikin hajjin abun da kuma ya
soma razanar da kampanonin hajina kasar Nijar.
Hukumomin kula da aikin hajjin na kasar Nijar da mu ka tuntuba sun
tabbatar da wadannan matsaloli to saidai a cewar kwamitin shirya aikin
hajji da umara na kasar ta Nijar ta bakin daya daga cikin mambobinsa
Malama Abdussamad Yahaya gwamnati na cikin fadin tashin shawo kan wanann matsalar.
Yanzu dai maniyatan kasar ta Nijar sun kashe kunne suna sauraran
dawowar ministan sufurin kasar ta Nijar daga kasar ta Saudiyya, domin
sanin makomar tafiyar ta su zuwa sabke faralin na shekarar bana.
A ƙasa kuna iya sauraron sauti ciki harda batun jigilar alhazan Najeriya
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman