Matsalar kudi a kasashen Turai
October 7, 2011An samu sabani tsakanin Jamus da Faransa kafin gudanar da taron koli a ranar lahadi wanda a yayinsa za a yi nazarin hanyoyin karfafa gwiwar bankunan Turai da yaki da yaduwar matsalar kudi a kasuwanni domin tsamo Girka daga matsalar bashi da ta tsunduma. Cewa aka yi Faransa ta mika bukatar kebe wani kudi daga asusun euro miliyan dubu 440 na ceto tattalin arzkin kasashen masu amfani da kudin domin ta zuba shi a bankunanta. Ita kuwa Jamus tsayawa kai da fata ta yi cewa ba zai yiwu an yi amfani da wannan asusu ba har sai daidaikun kasahen sun fuskanci matsananciyar matsalar rashin kudi. A baya ga Jamus Faransa ita ce kasa ta biyu da ta ba da tabbacin ga wannan asusu dake fuskantar yiwuwar rage matsayin bankunanta. Kuma hakan wani abu ne da ka iya kawo cikas ga shirin tallafa wa kasashen Girka da Portugal da Ireland. A ma jiya alhamis sai da shugaba Barack Obama yace matsalar kudi da kasashen Turai ke fuskanta na zaman babban barazana ga tattalin arzikin Amirka . A don haka yi kira ga shugabannin kungiyar Tarayar Turai da su lalubo hanyoyin magance wannan matsala.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi