Samun guraben karatu a kasashen ketare abu ne da ke yi wa wasu matasan Afirka wahala duk da sha'awar hakan da suke yi. A cikin wannan bidiyon, matashi Bishara Shettima Kuburi daga jihar Bornon Najeriya ya yi wa DW bayani kan yadda ya samu damar karatu a Jamus.