Me ya janyo matasa ke baya-baya da zaben Kamaru?
September 1, 2025Makwanni gabanin babban zaben Kamaru ya zuwa yanzu ba wasu takamaiman alamomin nuna zumudi ko shaukin zaben shugaban kasa daga bangaren wasu matasan kasar duba da yadda bangaren adawa suka kasa fitar da tilpon dan takara da zai iya kalubalanci Shugaba Paul Biya mais hekaru 92, kana uwa uba ma dai wasu matasan sun cire tsammani, tun bayan da kotun koli ta yi fatali da takarar babban abokin hamayyar Biya watau Maurice Kamto daga takara, wanda hakan ta sa tun ba a je ko ina ba wasu matasan suka cire tsammani na ganin sauyi, daga mulkin sai mahadi ka ture na Biya da ya share fiye da shekaru 40.
Karin Bayani:Kotun Kamaru ta hana Maurice Kamto shiga zaben shugaban kasa
Sai dai ba dukkanin matasan kasar Kamarun ba ne suka tattara suka yi watsi da siyasa da manufofin 'yan takarar ba a yanzu a daidai lokacin da zaben na 12 ga watan gobe na kara karatowa, wasu matasa da dama har yanzu suna kila-wa-kala, dangane da tanadin da suka yi wa zaben mai karatowa.
Wannan guda ne daga cikin matasan Kamaru da ke yin 'yan sana'o'in hannu kan titi, ya bayyana wa tahsar DW cewa yana bibiye da yadda harkokin siyasar kasar ke tafiya a halkin yanzu, to amma kuma yana cike da shakku. Sai dai shi kuwa jagoran matasa Florent Siewe, kira ya yi ga masu jinin a jika da ma kasashen duniya da su yi wa Allah su dubi yadda zaben na tafe zai kasance an yi shi da babban abokin hamayyar Paul Biya Maurice Kamto.
Har ya zuwa yanzu 'yan adawar kasar Kamaru ba su kai fitar da dan takara guda da zai iya kai rwau rana da shugaba Paul Biya ba, inda bangarori da dama ke yi wa batun kallon tamkar da akwai rashin yarda a tsakanin su.
Sai dai shugaban jam'iyyar MNP wata jam'iyyar mai zaman kanta a Kamaru, na ganin cewar rashin nuna zumudin matasa a babban zaben baya rasa nasaba da rashin kwarewar da suke da shi ta siyasa. Shugaba Paul Biya mai neman ta zarce kan mulkin dai duk da yake ba ya fitowa a fagen siyasar Kamaru ana ganin sa a zahiri a yanzu, na nuna alamun cewar zai ci gaba da jan zarensa domin kuwa ya bai wa abokan hamayya rata, a baya-bayan nan ma dai wasu shugabannin addinai da na sarakunan gargajiya ciki har da jiga-jigan 'yan adawa duk sun yi masa mubayi'a.