Matasa sun kai hari hedikwatar Human Rights na Kenya
July 6, 2025Matasa sun kai farmakin a daidai lokacin da hukumar ta kira taron manema labarai domin gabatar da jawabi kan batan-dabo da mutane ke yi da kuma daure mutane ba tare da an gudanar da shari'a ba.
Karin bayani:Yan sandan Kenya sun cafke daruruwan masu zanga-zanga
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da dubban matasan kasar suka shirya gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin 7 ga watan Yuli, 2025 domin tunawa da "Ranar Saba Saba" na yaki da tsadar rayuwa da jaddada dimukuradiyya da aka gudanar a 1990, wanda ya kawo karshen mulkin kama-karya na Daniel Arap Moi.
Karin bayani:Ruto na kenya ya yi kakkausar suka kan shirin zanga-zanga
Kasar Kenya na fuskantar kalubale mafi girma a baya-bayan nan da suka hadar da tashe-tashen hankula da cin hanci da rashawa da tsadar rayuwa da cin zarafin al'umma daga jami'an 'yan sanda duk dai a gwamnatin Shugaba William Ruto.