SiyasaAmurka
Amurka: Kotu ta yi watsi da katse agaji
March 5, 2025Talla
Karkashin hukuncin tilas gwamnatin Donald Trump ta ci gaba da bayar da kudin agajin, inda za ta biya kimanin dala milyan dubu biyu da ya dace a bayar lokacin da aka rufe asusun kula da agajin na Amurka. A shari'ar da aka yi dai alkalai biyar na kotun kolin sun rinjayi hudu, inda suka bukaci a koma da shari'ar karamar kotun da ta tilasta ci gaba da biyan kudin agajin, ga Hukumar Raya Kasashe ta Amurkan wato USAID. Tun farko karamar kotun ta bukaci a ci gaba da aiki da dokar kashe kudin hukumar kamar yadda dokokin kasar suka tsara, sai dai Shugaba Trump ya yi gaban kansa wajen saka hannu kan ayar doka wadda ba ta cika sharuddan dokokin kasar ta Amurka ba.