Isra'ila ta saki ɗaruruwan Falasdinawa
February 27, 2025Ofishin firaministan Isra'ila ya tabbatar da karbar gawwakin 'yan Isra'ila hudu daga kungiyar agaji ta Red Cross, daga cikin wadanda Hamas ke garkuwa da su tun watan Oktoba shekarar 2023.
Hakan dai na zuwa ne bayan da Isra'ila ta dakatar da sakin fursunoni Falalsdinawa sama da 600 a makon da ya gabata.
Tuni dai aka garzaya da gawwakin hudu na 'yan Isra'ila don gudanar musu da gwajin kwayoyin halitta, don tabbatar da cewa gawawwakin na wadanda Hamas din ta shelanta za ta sako ne.
Kamar yadda ita ma a nata banagaren, kungiyar Hamas ta ce,tun da safiyar Alhamis (27.02.2025) ne,motocin safa-safa daga gidan jarum na Obar da ke Isra'la suka kwaso daruruwan Falalsdinawa zuwa yankin Gabar Yamma da Kogin Jodan.
A gobe Juma'a ne (28.02.2025),tawagogin tattaunawa na bangarorin biyu za su isa birnin Doha na kasar Qatar don fara tattaaunawa kan yadda zagaye na biyu na yarjejeniyar da za ta kai ga dakatar da yakin na din-din-din a Gaza da sako sauran wadanda Hamas ke garkuwa da su su 65.