Najeriya zata tsaurara matakan tsaro
January 17, 2019Domin baya ga matsalolin da ake fuskanta a jihohi irin na Zamfara da Kaduna da a yanzu yake naso zuwa Katsina, dauki dai dai a lokacin yakin neman zabe da aka gani a Lagas na tada hankali.
Duk da daga hankalin da ake yi a game da batun tsaro ga Janarl Abdurrahman Dambazau ministan kula da harkokin cikin gida da ya yiwa taron ‘yan jaridu bayani a Abuja, ya ce akwai bukatar duba yadda suka samu kasar.
Batun halin da kan iyakokin Najeriyar ke ciki dai da aka dade da yi wa kalon wanda bakin haure ke shigowa sakakai a kai ya kasance wani muhimmin batu na tsaro ba kawai a lokacin zabe ba, domin koda a watanin baya said a aka fatataki wasu baki da aka dangatanta su da mahara a jihar Sokoto. Amma ga Mohammed Baban Dede babban comptroller na hukumar kula da shige da ficen jama'a, aikin da suke tukuru ya kaisu ga samun nasarar kame bakin haure da suka so shigar burtu da yin zabe a kasar.
Sauran hukumomin tsaro kama daga ‘yan sanda zuwa na rundunar tsaro ta fararen kaya watau Civil Defense, duka sun bayyana shirin da suka yi.