Matakan saukaka zirga-zirga tsakanin kasashen AES
January 24, 2025Ministocin kula da harkokin gine-gine na kasashen AES da suka Nijar da Mali da Burkia Faso, sun yi wani zama a birnin bamako na kasar Mali inda suka tattauna batutuwa da suka shafi gine-ginen manyan hanyoyi na kasa da kasa da ma batun shinfila lafin dogo a wani mataki na saukaka zirga-zirga tare da gurguso da mannyan biranen kasashen uku kusa da juna ta hanyar wadannan hanyoyi da za a gina. Sai dai kuma an jima ana daukan iri-irin. Wadannan manyan alkawulla ba tare da cikawa ba.
Tun dai a ranekun 16 zuwa 18 ga watan nan ne na Janairu ministaocin kula da harkokin gine-gine tarer da sauran kwararru ne suka yi zama na musamman domin duba yuyuwar wannan katafaran tsari na samar da hanyoyi na kasa da kasa na Express da za su hada biranen Bamako, Ouagadoudou da kuma birnin Yamai, sannan da tsarin samar da lafin dogo da shi ma zai hada biranen uku na kasashen AES da kuma birnin Kaya a Burkina Faso zuwa Lome babban birnin kasar Togo.Tuni daim asana ke. Kallon wannan tsari a matsayin wata daga da za a bai way an kasuwa da sauran al'umma ta yankin na AES. Farfesa Dicko Abdourahamane na da iri wannan tunani :
Ganin cewa a baya dai an sha jin irin wadannan batutuwa na samar da layin dogo daga Burkina Faso zuwa Nijar ko babbar hanya ta daga Algeriya zuwa cikin Nijar har ta je Najeriya amma ba tare da an ga zahiri ba, ko ta yaya shi wannan tsari na yanzu na kasashen AES zai iya gamsar da al'umomin.
Ba yau ba ne dai ake ruwa kasa na shanyewa, domin kuwa an jima ana jiran iri-iri wadannan ayyuka koda tsakanin kasa da kasa amma sama da shekaru 60. Da samun. Mulkin kai babu ingantattun hanyoyi a ciki kasa iri su Nijar, wanda a cewar Sherif Haidara wani dan Nijar da ke Faransa fatansu dai shi ne su ga zahiri a wannan karo.
Baya ma ga batun na hanyoyi, zaman taron ministocin na AES ya ba da damar tabbatar da taswirar hanyoyin da suka shafi samar da Bankin zuba Jari ta kasashen na AES wanda shi ma tsari neda ahalin yanzu aka aminta da shi kuma zai wakana ba da wani dogon lokaci ba.