Matakan Nijar game da rashin kyaun damuna
September 9, 2011Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar wa duniya bukatar ta ta neman agaji sakamakon fargabar da ke tattare da ita dangane da tafiyar hawainiya da damuna ke yi a wannan shekara ta 2011. Alƙalumman hukumar ayyukan noma ta ƙasa su nunar da cewar ya zuwa yanzu kashi 85% na amfanin goma ya salwanta sanadiyyar rashin wadataccen ruwan sama a wasu yankunan Nijar, da kuma bayyanar da ƙwari da tsutsa suka yi a wasu yankunan tare da lalata cimakar da ta kama hanyar nuna. Ko shi ma Seidu Ama, wani ɗan majalisar dokoki , sai da ya tabbatar da matsalar ta lalacewar shuka a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido halin da manoma ke ciki a jaharsa ta asali.
To sai dai masana ilimin tattalin arziki da kuma zamantakewa a yankunan karkara na Nijar sun bayyana cewar akwai hanyar da gwamnati za ta iya bi domin magance wannan matsala ta ƙarancin abincin da za a iya fiskanta. Dokta Abarshi Magalma na ɗaya daga cikin masu wannan ra'ayi. Tuni dai gwamnati Mahamadou Issoufou ta bayyana matakai na ƙashin kanta da za ta dauka domin rage kaifin matsalar lalacewar shuka da ake fiskanta. Kana fadar mulki ta Niamey ta fara miƙa lamarin a hannun ubangiji inda ta bukaci a gudanar da sallar roƙon ruwa ta gama gari a ƙasar, da zummar ganin mai kowa da komai ya sawwake halin rashin tabbas da damuna ta shiga a Nijar.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasaawa
Edita: Mouhamadou Awal