Nijar: Karbuwar tsarin iyali
November 12, 2019Hukumomi a kasar ta Nijar sun tabbatar da irin ci gaban da aka samu a batun tsarin iyali da aka kwashi tsawon lokaci ana fafutukar fadakar da jama'a alfanunsa. Rahotannin gwamnati sun nunar da cewa, yanzu an sami raguwar yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara jarirai.
A Yamai babban birnin kasar, ana ci gaba da yi wa mata huduba don su fahimci mahimmancin yin tazara a tsakanin haihuwa, duk da cewa an gano yadda mata ke saka shekara akalla biyu ko uku a tsakanin haihuwa, jami'an kiwon lafiya na ganin, akwai sauran aiki a gaba, kafin a kai ga kawar da matsalar mace-macen mata a yayin haihuwa.
Hukumomin sun ci gaba da aiki tare da malaman addinai da sarakunan gargajiya, ta yadda zasu taimaka musu da wayar da kan mata mahinmancin sa tazara a tsakanin haihuwa da kuma bin tsarin iyali na kayyade iyali.