Harajin Trump ya gigita kasuwannin hannun jari a Asiya
July 15, 2025Wasu alkaluma sun yi nuni da cewa kasuwar danyen mai na ci gaba da faduwa a yankin Asiya, sannan wa'adin kwanaki 50 da shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa Rasha domin kawo karshen yakin Ukraine ya sanyaya gwiwar masu zuka hannun jari.
Da misalin karfe uku da kwata na ranar Talata agogon GMT, gangan mai na Amurka da ake kira WTI ya yi asarar kashi 0,46% inda ake sayar da shi a kan dala 66,67 sannan gangan mai na Brent shi kuwa ya ja baya da kashi 0,38% inda ake sayar da shi zuwa dala 68,96.
Karin bayani: Trump ya lafta wa EU sabon haraji, von der Leyen ta lashi takobin mayar da martani
A gefe guda masu saka hannun jari a wannan yanki da ke da kasuwa mai fadin na shakku dangane da sabon matakin Donald Trump wanda a ranar Asabar da ta gabata ya yi barazanar kara haraji na kashi 30% ga Mexico da kuma Tarayyar Turai, karin da zai fara daga ranar daya ga watan Ogusta mai zuwa.