SiyasaAfirka
Masu ikirarin jihadi sun kashe mutane 55 a arewacin Najeriya
September 6, 2025Talla
Shaidun gani da ido sun sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mayakan sun kai farmaki kauyen Darul Jama da ke kasancewa sansanin sojojin Najeriya da Kamaru da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kan iyakar kasashen. Mazauna yankin sun sanar da cewa sojoji biyar na daga cikin mutanen da mayakan suka kashe, yayinda kwamandan rundunar Babagana Ibrahim ya sanar da cewa adadin sojojin da suka mutu sun kai shida.
Karin bayani:Yan ta'addan IS sun halaka manoma 15 a Arewacin Najeriya
Mayakan Boko Haram da ke da'awar kafa daular Islama a Najeriya da sauran kasashen Sahel sun kaddamar da hare-hare tun a shekara 2009, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 40,000 yayinda mutane sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu.