SiyasaTurai
Masu adawa da Isra'ila sun mamaye bikin fina-finan Venice
August 27, 2025Talla
Masu zanga-zangar dauke da allunan da ke cewa ''a tabbatar da 'yancin Falasdinu' da kuma 'kawo karshen kisan kare dangi a Gaza' da makamantan rubuce-rubuce sun yi cincirindo a dandalin gudanar da bikin fina-finan Venice na Italiya, inda al'amura suka tsaya cak!
Karin bayani:Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Yemen
Fim din da aka shirya kan rayuwar wata yarinya 'yar shekara shida mai suna Hind Rajab, da sojojin Isra'ila suka halaka a 2024 na daga cikin fina-finan da suka shiga gasar samun lambar yabo ta 'Golden Lion' a gasar ta bana, kamar yadda daraktar da ta shirya fim din Kaouther Ben Hania ta sanar da manema labarai.