Masar ta yi canjaras da Burkina Faso a kwallon kafa
September 10, 2025Talla
Kawo yanzu, kasashen Morocco da Tunisiya su ne kadai daga Afirka da suka riga suka samu gurbi a gasar mafi daukaka a kwallon kafar duniya.
A rukuni na C, Afirka ta Kudu ta yi fatan samun tikiti amma za ta ci gaba da jiran sanin makomarta bayan wasan da ta yi da Najeriya da aka tashi ci 1–1 a tsakaninta da Najeriya.
Wannan sakamako ya sa kungiyar Super Eagles ta Najeriya cikin hatsarin rasa halartar gasar duniyar a karo na biyu a jere, duk da tana da manyan 'yan wasa da ke bugawa a Turai, irin su Victor Osimhen da kuma gwarzon dan kwallon Afirka, Ademola Lookman.