Masar da Qatar na matsa kaimi don tsagaita wuta a Gaza
June 1, 2025Kasashen da ke shiga tsakani a yakin da Isra'ila ke yi a Gaza sun bayyana cewa har yanzu suna dukkan mai yiwuwa don ganin an tsagaita wuta a zirin mai fama da rashin abinci sakamakon yaki.
Masar da Qatar sun sanar a ranar Lahadi cewa suna sauraron ra'ayoyin bangarorin Hamas da Isra'ila domin ganin an warware duk wata takddama da ake fuskanta.
Ina mafita ga Zirin Gaza na Falasdinu?
Suka ce sun fitar da sanarwar ce bisa la'akari da daftarin da Jakadan Amurka a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff ya gabatar wanda Isra'ila ta amince da shi a yayin da Hamas kuwa ta yi watsi da daftarin.
A cikin sanarwar ta hadin gwiwa tsakanin kasashen da Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta sanya wa hannu, kasashen sun bukaci dukkan bangarorin su goyi bayan masu shiga tsakani don kawo karshen yakin.
MDD ta kadu kan yawan mutane da ke bukatar agaji a Gaza
Ko da a ranar Lahadi, hukumomi a Falasdinu sun ce Isra'ila ta halaka mutane 31 da suka je karbar kayan agaji a zirin na Gaza.
Ko da yake sojojin Isra'ilar suka ce hotunan da suka gani ta sama sun nuna wasu mutane masu fuskoki a rufe ne suka yi harbi kan fararen hula da ke kokarin karbar abinci a Gaza.