Martin Kobler, sabon shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Kongo
June 10, 2013Talla
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Ban Ki-Moon ya nada Bajamushe Martin Kobler a matsayin shugaban tawagar majalisar da ke shiga tsakani a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo. Kobler, wanda yanzu ke rike da mukamin wakili na musamman na MDD a Iraki zai amshi ragamar wannan aiki a can Jamhuriyar Demokradiyar Kongon ne daga hannun Roger Meece, wanda zai bar kasar a watan Yuli.
Bajamushen, wanda ya taba rike mukamin shugaban majalisar minisotici wa tsohon ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer ya samu gogewar shekaru 25 na aikin diplomasiya, da ya hada da yin aiki da MDD a Afganistan da kuma wakiltar Jamus a kasashen Iraki da Masar.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal